Baya ga lakabin suna da akayi ma matashi Mamoudou na “Spider Man” biyo bayan wata bajinta da yayi ta hawa wani bene a birnin Paris don ya ceto wani yaro da ya zame ya kusa fadowa daga bene ya na lilo a wani gidan bene mai hawa hudu.
Mamoudou Gassama, mai shekaru 22 da haihuwa ya ce ya ga yaron na cikin mummunan hali a unguwar da ya je ranar Asabar don kallon wasan kwallon kafa a wani gidan saida abinci.
Gassama ya fadawa sashen Bambara na muryar Amurka cewa, sun yi odar abinci kenan shi da budurwarsa, sai suka ga mutane sun tattaru.
Ya ce “kafin mu fara cin abinci, na ga mutane a waje. Wasu na ihu, direbobi kuma na ta latsa horn din mota. Sai na fita waje, na ga yaron yana lilo a saman bene na hudu, matashin ya kara da cewa “na godewa Allah yadda na iya kama karafuna ta gaban benen, na hau don in ceto shi, da na fara hawa karafunan, sai na kara samun kwarin guiwar ceto yaron.
Bayan da ya ceto yaron sai ‘yan sanda suka tare su ta wani daki, matashin ya kara da cewar “sai na fara makayarkyata, na kasa tsayawa, nayi ta rawar jiki saboda abinda ya faru.
Da farko ya fadawa CNN cewa yana son yara. Ba zan so in ga yaron ya ji rauni ba a gaban ido na. sai na ruga don neman hanyar da zan ceto shi. Na godewa Allah yadda na iya hawa ta gaban benen har na taddo yaron.
Daga bisani shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya gayyaci matashin inda suka gana kuma ya bashi takardar zama dan kasa kana da aiki a ma'aikatar 'yan kwanakwana, duk a dalilin jarumtaka da yayi.