Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Iyaye Sun Shigar Da Dan Su Mai shekaru 30 Kara Kotu A Dalilin...


Wasu iyaye mazauna karamar hukumar Onondaga ta jihar New York, a kasar Amurka, sun shigar da dan su kara a babbar kotu, inda suke bukatar dan nasu mai shekaru talatin 30, ya tashi ya bar masu gidan su, don ya kamata ace yana zaman kansa a wadannan shekaru.

Takardun kotun sun nuna cewar Mr. Michael Rotondo, baya biyan iyayen sa kudin haya, ko kuma taimaka masu wajen gyaran gida da wasu aikace akace, hakan yasa suka bukaci ya tashi yaje ya nemi nashi gidan inda zai rika biyan kudin haya.

Matashin dai ya yi kunnen uwar shegu da bukatar iyayen nasa, inda suka bashi takardar kora sau uku, amma bai dauki wani matakin tashi daga gidan iyayen nasa ba.

Hakan yasa suka garzaya babbar kotu dake kusa da kauyen Syracuse, dake birnin New York, don kai dan nasu kara, inda kotu ta bukaci jin ta bakin dan nasu, wanda ya bayyana cewa shi ba’a bashi takardar kora da wuri ba.

A wasikar da iyayen suka rubuta ma dan nasu na kunshe da cewar “Dole ka fita daga gidan nan cikin gaggawa, bamu da bukatar zama da kai cikin gida daya” a wasikar ta uku sun shaida masa cewar idan har bai fita daga gidan ba, zasu gurfanar da shi gaban kuliya, wasikar na dauke da sa hannun mahaifiyar yaron Mrs. Rotondo ta kai gare shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG