Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigar Amaryar Yariman Ingila Babu Kamarta A Duniya


Bayan kammala bukin da aka gudanar a gidan sarauniyar Ingila, inda jikan Sarauniya Queen Elizabeth ll, Yarima Harry yayi wanda yake cike da dinbin tarihi, domin kuwa a karon farko da wata jinsin bakar fata ta shiga cikin dangin masarautar kasar Ingila.

Duk da cewar gidan sarautar nada dinbin tarihin shekaru da dama, Yarima Harry ya auri tsohuwar tauraruwar 'yar wasan fina-finan Amurka Meghan Markle, wadda a karon farko suka fitar da hotunan bukin. An kiyasta kimanin mutane sama da milliyan talatin suka kalli bukin.

Rigar da amaryar ta saka a ranar bukin, riga ce da ba’a taba dinka irinta ba don wani buki, domin kuwa wani shahararren kamfani aka ba kwantirakin dinka ta, kamfanin Givenchy” ya dinka rigar, wanda aka kwashe watannin biyar ana zanawa kafin a dinka.

Su kansu mutanen da suka dinka rigar basu da masaniyar rigar ko ta wacece, an dinka rigar a kasar Faris, inda aka kayata mayafin rigar da filawowin duk kasashe renon ingila, wannan rigar sai amarya Meghan.

A cewar madinkin rigar mahaifiyar Yarima Harry, lallai anyi hikima matuka wajen saka filawowin kasashe renon Ingila wajen dinka mayafin rigar, domin kuwa koda mahaifiyar ango na raye zata ce wannan tsarin yayi.

Angon ya ba amaryar sa kyautar wani zoben tagulla da ya gada a wajen mahafiyar sa Diana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG