Rade radi sun cike kafafen yada labarun Najeriya, masamman ma jaridar “Thisday” kan ziyarar da shugaba Buhari zai kai Amurka, da ake cewa za’a bujuro da batun neman Najeriya, ta amince da auren jinsi daya.
Jaridar ta ruwaito cewa mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka, mai kula da nahiyar Afirka, Linda Thomas Greenfield, a cewar Amurka, zata yi kokarin ciwo kan Buhari, ya matsawa majalisar dokoki ta amince da ‘yancin masu son auren jinsi daya.
Dan wannan kudurin mutunta hakokin ‘yancin ‘yan Adam ne da Amurka, ke son yadawa a dukan duniya.
Amma a nasa bangaren babban mai taimakawa shugaban Najeriya, akan Labaru Fema Adeshina, yace ziyarar da Buhari zai kai Amurka, da kuma ganawa da shugaba Obama, ta shafi harkokin tsaro da tattalin arziki ne.