A baya, jagoran yan bindigar da ake kira Dogo Gide da kan baiwa daliban damar magana da iyayensu ta waya, yanzu ya ce ba zai kara barin daliban su ke magana da iyayensu ba.
Tun farko dai dan ta’addan ya ce ba ruwansa da iyayen yaran, sai dai gwamnati. Amma a ranar Lahadi dan ta’addan ya ce ya amince iyayen yaran su harhada masa Naira miliyan Dari a matsayin kudin fansa don karbar yaran su.
A halin da ake ciki yanzu, tuni iyayen yaran suka zauna wani taro, inda suka yanke shawarar sayar da kaddarorinsu da su ka hada da gidaje da gonakinunsu don tattara kudin da zasu fanso yan matan.
Jagoran iyayen daliban dake yin waya da dan bindigar Salim Sani ka’Oje, ya shaidawa muryar Amurka cewa jagoran yan bindigar Dogo Gide ya gargade su cewa muddin basu kai masa Naira miliyan dari ba, to shi kenan sun rabu da ya’yan su kenan har abada.
Da yake magana da sashin Hausa, wani kwararren lauyan tsarin mulki a Najeriya Barrister Yakubu Sale Bawa, ya ce ba wata ayar doka a kundin tsarin mulkin Najeriya, da yai magana akan biyan kudin fansa, don haka in har sun harhada kudin to ba wanda zai ce sunyi laifi.
Domin karin bauyani saurari rahotan Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5