Bashin Ghana Ya Karu Da Kashi 20% A Cikin Watanni Hudu

Bankin kasar Ghana

Basusukan da ake bin kasar Ghana sun karu da kashi 20 cikin 100, zuwa GHC biliyan 569.3 (kimanin dalar Amurka biliyan $50) a karshen watan Afrilu 2023, idan aka kwatanta da GHC biliyan 434.6 da ake bin kasar a karshen watan Disambar 2022, inji Bankin Ghana a shafinsa na yanar gizo.

Hakan na nufin cewa an sami karuwar GHS biliyan 134.7 a cikin watanni hudu na farkon shekara, wanda wasu masharhanta suka ce zai kara ta'azzara matsin tattalin arziki da gudanar da ayyukan ci gaba a kasa.

Malamin tattalin arzikin kasa da harkokin kudi a jami’ar Islamiya ta Ghana, Nuhu Eliasu yace karin yawan basussukan da ake bin kasar zai sa kasashe da hukumomin da ke baiwa Ghana rance su janye, domin gudun kada ta kasa biyansu.

Yace har ila yau kuma, gwamnati ba zata iya gudanar da wasu ayyuka masu muhimmanci ba, domin kudade da kasar ke hadawa na cikin gida ba za su isa gudanar da ayyukan ba.

Bankin Ghana ya takaita yadda basussukan suka dinga karuwa a jere daga watan Janairu zuwa Maris 2023, wanda ya kai GHS biliyan 547.8 (dala biliyan 50.7) a Janairu, GHS biliyan 564.1 (dala biliyan 51.2) a Fabrairu, da kuma GHS biliyan 569.3 (dala biliyan 51.7) a watan Maris.

Kamar yadda bankin ya ce hakan ya samo asali ne sakamakon faduwar darajar cedi a cikin wannan lokacin, da kuma fadada basussukan cikin gida da aka yi, wanda ya kai GHC biliyan 15.9, wanda hakan ke bukatar gwamnati ta aiwatar da matakan magance kalubalen kasafin kudi.

Sarki Imrana Hashiru Dikeni, mai sharhi kan tattalin arziki ya ce daga cikin hanyoyin da za'a shawo kan lamarin shi ne a kara habaka sarrafa kayayyakin cikin gida kuma ‘yan kasa su sayi wadannan kayayyakin.

Ya kara da cewa , idan aka yi hakan, zai haifar da raguwar bukatar dalar Amurka don sayen kayayyakin kasashen waje zuwa cikin kasar.

Eliasu Nuhu a nasa bangaren, ya ce kamata yayi gwamnati ta rage kashe kudade, kuma ta ilmantar da al’umma game da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Bankin ya kasafta basussukan da cewa: bashin kasashen waje ya karu zuwa GHC biliyan 321.4 a karshen watan Afrilu daga GHC biliyan 240.9 a watan Disamba. Bashin cikin gida kuma ya karu zuwa GHC biliyan 247.9 daga GHC biliyan 232.3 a tsawon watanni hudun.

Saurari rahoton Idris Abdallah a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Bashin Kasar Ghana Ya Karu Da Kashi 20% A Cikin Watanni Hudu