Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Lakume Dala Miliyan 560 Wajen Shigar Da Shinkafa Daga Ketare


Taron manoman shinkafa
Taron manoman shinkafa

A wani bangare na bada gudummuwa wajen ganin Ghana ta shawo kan matsalar abinci, kasar Isra'la ta shirya wani taro tsakanin manoman shinkafa a Ghana da na kasarta a birnin Accra, inda suka tattauna kan matakai da dama.

Wani rahoto da kungiyar IDH Sustainable Trade Initiative, kungiyar da ke fafutukar karfafa kasuwanci mai dorewa tsakanin kasashe ta fidda kwanan nan, ya nuna cewa Ghana ta lakume dala miliyan 560 wajen shigar da shinkafa daga kasashen waje a shekarar 2022.

Lamarin da masu sharhi suka ce yana barazana ga abinci da kuma kokarin da kasar ke yi wajen shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da take fama da shi.

Taron manoman shinkafa
Taron manoman shinkafa

Jafar Dankwabiya, mai sharhi kan harkokin noma kana babban jami'i a hukumar da ke nazari a kan shuka ta kasa, ya bayyana wasu dalilai da a ganinsa ke ci gaba da sanya kasar dogaro ga kasashen ketare domin shigar da shinkafa.

"Duk wanda ya san noman shinkafa ya san cewa yana bukatar ruwa sosai fiye da taki kuma sama da kashi saba'in cikin dari na manoma a Ghana na dogara ne a kan ruwan sama don noman, a cewar Dankwabiya.

Ya kara da cewa abu na biyu kuma, manoma na amfani da irin da kakanninsu suka yi amfani da su shekaru fiye da 30 da suka shude maimakon amfani da iri na zamani da zai samar da amfani da yawa.

Manoma a kasar basu da karfin sayen takin zamani su kuma 'yan kasa sun fi son shinkafar da aka shigo da ita daga ketare saboda ta fi ta cikin gida dadi, a cewar Dankwabiya."

noman shinkafa
noman shinkafa

Shi kuwa mai sharhi kan tattalin arzikin kasa Dakta Najeeb Ibn Hassan, ya bayyana cewa amfani da kudaden kasar waje musamman dalar Amurka da Ghana ke yi wajen sayo shinkafa daga ketare na daya daga cikin dalilan da suka sa kasar ke ci gaba da fama da matsalar faduwar darajar Sidi a kan dalar Amurka.

"A duk lokacin da kasa bata iya ciyar da kanta da abincin da take nomawa cikin gida abin damuwa ne sosai, saboda yin hakan na daga cikin dalilan da ke sa kudin Ghana wato Sidi ke ci gaba da faduwa, don a duk lokacin da za a sayo abinci daga ketare ana bukatar dalar Amurka. Lamarin da ke takura wa babban banki kasa saboda dole sai ya fitar da kudade ya ba masu shigo da shinkafa daga waje," inji Ibn Hassan.

Taron manoman shinkafa
Taron manoman shinkafa

A wani bangare na bada gudummuwa wajen ganin Ghana ta shawo kan matsalar abinci, kasar Isra'ila ta shirya wani taro tsakanin manoman shinkafa a Ghana da na kasarta a birnin Accra don tattaunawa kan matakai da dama.

"Mun shirya wannan taro ne domin taimakawa tare da samar da matakan magance matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi da suka shafi noma ta hanyar fasahar zamani da kirkire-kirkire," abin da jakadiyar Isra'ila a Ghana Shlomit Sufa ta fada wa manema labarai kenan.

Ta kara da cewa wannan matakin zai yi tasiri a Ghana da ma nahiyar Afrika gaba daya. Saboda zai bai wa Ghana damar yin dogaro da kai tare da bada gudummuwar cimma muradan ci gaba masu dorewa na majalisar dinkin duniya.

Wasu mahalarta taron sun nuna farin cikinsu bisa wannan mataki da kasar Isra'ila ta dauka na taimakon Ghana, inda suke cewa hakan zai taimaka wa kasar sosai ta zama mai dagora da kai.

Saurari rahoton Hamza Adams a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG