Barrack Obama Ya Umarci Matasa Suyi Gwagwarmayar Kafa Dimokradiya

Barack Obama

Barack Obama

Barrack Obama ya ce akwai amfani tattare da zaman lumana tare a tsakanin al'uma masu akidu da addinai daban-daban, kuma masu launin fata dabam daban.

Tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama, yayi tattaki zuwa Jakarta, babban birnin Indonesiya, kuma birnin da yayi zama cikinta lokacin da yake karamin yaro, domin gudanar da wani jawabi na Taron ‘Yan Indonesiya dake zaune a kasashen ketare.

Obama ya kwatanta Amurka da Indonesiya wadanda suke tattare da kabilu daban-daban dukkansu, ya kuma yi kira ga matasa da su yi gwagwarmayar ganin an kafa dimokuradiyya. Yayi Magana sosai a kan amfanin dake tattare da zaman lumana tare a tsakanin masu akidu da addinai dabam-dabam, kuma masu launin fata dabam dabam.

Wannan taron da yayi Magana a wajensa yau asabar, an shirya shine domin hada kan Indonesiyawa daga kowace kusurwa ta duniya. Wadanda suka shirya taron sun ce an samu mahalarta daga kasashe 55.