A jahar Nija, an kashe akalla mutane hudu a yankin kontagora, a wata arangama tsakanin mutanen gari da ‘yan banga.
Wani da aka yi lamarin kan idonsa mai suna Mohammed Nura Usman, ya gayawa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa, wasu ‘yan banga ne suka kama wani matashi bayan da aka tashi daga kallon kwallo bisa zargin aikata wani laifi da ba’a fayyace ba. Suka rika yi masa duka har sai da ya mutu.
Bayan da aka dawo da gawarsa, mutanen unguwar suka fusata, suka yi zanga-zanga har zuwa ofishin ‘Yan bangan har suka kona ofishinsu.
A nasu maratnin, inji Nura, ‘yan bangan suka je gidan da matashin nan yake da zama, suka rika jifa suna hayaniya, suka kuma bude wuta kan mazauna gidan suka harbe matasa uku da mace daya.
Kakakin rundunar ‘Yansanda na jahar DSP Bala Elkanah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace zuwa yanzu basu da adadin wadanda rikicin ya halaka. Domin jami’ansu suna ci gaba da aiki a yankin.
Facebook Forum