An baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin mako daya ta maidawa wakilin Sashen Hausa na gidan Rediyon Deutsche Welle a Kaduna Ibrahima Yakuba, kayan aikinsa da aka lalata.
Wata kungiyar kare ‘yancin Bil’Adama da ake kira da cibiyar wanzarda zaman lafiya da adalci a Afirka wacce ta bada wannan wa’adi, tace bai kamata a rika cin zarafin ‘Yan jarida ba.
Shugaban cibiyar Dr. Suleiman Shu’aibu Shinkafi, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai da kngiyar ta kira a Jos yace, ‘yan jarida sune ido da bakin talakawa.
Ana zargin wakilin ya hadu da fushin ‘Yansanda a kaduna, lokacinda yake daukar bayanai a wata zanga-zanga da take son ta rikida ta zama arangama tsakanin ‘yan shi’a da jama’ar gari.
Shima da yake magana, shugaban kungiyar ‘yan jarida reshen jahar Flato Yakubu Tadi, yace akwai bukatar uwar kungiyar ta kasa ta sa baki cikin wannan batu. Domin idan ba haka ba, wannan somin tabi ne kamin shekara ta 2019 lokacinda za’a yi zaben kasar.
Facebook Forum