Sevilla ta maku a hannun Barcelona da ci 2-0, inda Lionel Messi da Ousmane Dembele suka zira kwallo guda-guda.
Barcelona ta kwashe makonni tana fuskantar komawa baya a gasar ta La Liga, wannan ce kuma nasararta ta tara cikin wasanni 10, abin da ke nuni da cewa tagomashinta ya farfado.
Hakan na nufin maki biyu kenan yake tsakaninta da Atletico Madrid wacce ke da wasanni biyu da za ta buga a nan gaba. Za ta buga daya ne da Villarreal a ranar Lahadi.
Sannan a karshen mako mai zuwa Sevillan wacce ke saman teburin gasar za ta kara da Real Madrid.
Sevilla ta fara wasan ne da kuzarin gaske, domin ta lashe wasanni shida a baya, inda biyar daga cikinsu ba a zira kwallo ko daya a ragarta ba.
Amma daga baya jaruman Ramon Sanchez Pizjuan, sun yi la’asar saboda irin taka leda ta kwarewa da Barcelona ta nuna.
Bangarorin biyu za su sake haduwa a ranar Laraba a zagaye na biyu a gasar Copa Del Ray inda Barcelona za ta yi kokarin rama ci 2-0 da Sevilla ta yi mata a Camp Nou.
Yanzu Atletico Madrid ce ke jagorantar teburin gasar ta La Liga da maki 55, Barcelona tana biye da ita da mai 53 sai Real Madrid mai maki 52 a matsayi ta uku yayin da Sevilla ke matsayi na hudu da maki 48.
Your browser doesn’t support HTML5