Masu sharhi kan kwallon kafa na ganin rabon da kungiyar ta fuskanci irin wannan koma baya tun bayan shekara 100 da suka gabata.
Kaye da ta sha na baya-bayan nan shi ne a hannun Everton, wacce ta bi ta har filin wasanta na Anfield ta doke ta da ci 0-2.
Rabon da Everton ta samu kan Liverpool a gida tun a shekarar 1999.
Tarihi dai ya nuna Liverpool ta fi Everton yin fice a fagen wasa, inda ta taba lashe kofin zakarun nahiyar turai shida, yayin da ta lashe kofin league din Ingila 19. A halin yanzu ma ita ke rike da kofin gasar ta Premier.
Wannan lamari ya sa masu fashin baki yin tsokaci kan dalilin da ya sa kungiyar wacce take tunkaho da jarumta wajen murkushe abokanan hamayya ta koma kashin baya.
Wasu na ganin rashin sa’ar da ya samu kungiyar, ya hada har da rashin ‘yan wasa masu tsaron gida irinsu Virgil Van Dijk da yake jinya da kuma Joel Matip.
Hakan ya sa, a cewar masanan, kocin kungiyar Klopp ya sake fasalin ‘yan wasansa don ya yi amfani da ‘yan wasansa na tsakiya don ya yi faci-faci a tsaron gidansa.
Yanzu Liverpool na matsayi na shida da maki 40 yayin da Everton ke biye da ita da maki 40 amma yawan kwallaye ya raba su inda Liverpool take da kwallaye five da na Everton a gasar ta Premier.