Yanzu kungiyar ta Inter ba da tazarar maki hudu a tsakaninta da AC Milan a gasar kenan.
Dan wasan Inter Lautaro Martinez ne ya zira kwallaye biyu yayin da Romelu Lukaku ya ci kwalla guda.
Lukaku ya ci kwallonsa ta 17 kenan a wannan kakar wasa, abin da ya ba shi damar darewa saman teburin ‘yan wasan da suka fi yawan kwallaye a gasar ta Serie A.
Kwallon farko da Martinez ya zira ita ta karawa Inter kwarin gwiwa kafin daga bisani ya zira ta biyu.
Sau biyu Zlatan Ibrahimovic ya yi yunkuri zira kwallo a ragar Inter amma abin ya cutura saboda jajircewa da Inter ta yi.
Wannan shi ne karo na biyu da bangarorin biyu suka hadu a daidai lokacin da suka kasance kungiyoyi na sama-sama da ke saman teburin gasar tun bayan shekarar 2011.
Yanzu Inter na da maki 53, AC Milan na biye da ita da maki 49, sai Roma da maki 44 a matsayi na uku, sannan sai Atalanta mai maki 43 da kuma Lazio da maki 43 a matsayi na biyar.