Wani kutsen yanar internet na kasa da kasa ya kawo tangarda ga harkoki a yau Laraba, a tasha mafi girma ta jiragen ruwan dakon kaya a Indiya, al'amarin da ya dada kawo damuwa ga gwamnatoci da harkokin kasuwanci, da ke fuskantar barazanar abin da ake kira, manhajar kutsen neman kudin fansa, wadda akan yi amfani da ita wajen kwace bayanan wadanda abin ya shafa, har sai sun biya kudin fansa kafin a maida masu.
Wannan matsalar da ta auku a tashar jirgin ruwa ta Jawaharlal Nehru da ke Mumbai, ta rutsa da bangaren babban kamfanin jirgin ruwan nan na Denmark, wanda ake kira A.P. Moller-Maersk. Kamfanin ya fadi jiya Talata cewa dayake kutsen na yaduwa sosai a Turai da Amurka, to lallai wannan mummunar manhajar na nan na barna ma tasoshin jirgin ruwa da dama.
Ministan ayyukan dakile kutsen internet na Australia, Dan Tehan, ya gaya ma manema labarai yau Laraba cewa har yanzu jami'ai ba su tantance ko waccen manhajar kutsen ce aka kai hari da ita kan wasu kamfanonin Australia biyu ba, to amma alamu da nuna hakan.
Bankuna da ofisoshin gwamnati da filayen jiragen sama a Ukraine na daga cikin wadanda su ka fara bayyana cewa sun fuskanci harin manhajar kusten.