Bankin Duniya Ya Sa Jamhuriyar Nijar A Sahun Kasashen Da Suka Sami Ci Gaban Tattalin Arziki A Afirka

Mahamadou Issoufou, shugaban kasar Nijar dake shirin barin gado.

Kasashen Afurka a kalla 10 ne kasar ta Nijar ta yi wa fintikau akan maganar ci gaban tattalin arziki a cewar rahoton na bankin duniya a bisa la’akari da karuwar yawan kudaden shigarta a bana, inda aka kyasta cewa an sami shigowar billion ko milliard 14. 3 na dollar Amurka kwatankwacin dala 567 da kowane dan kasar ke samu a kowace rana. Masanin tattalin arziki Dr Soly Abdoulaye ya yi sharhi akan wannan rahoto.

kasuwar Falla, dake jihar Tillaberi, a jamhuriyar Nijar


Shekaru aru aru jamhuriyar Nijar ke rike matsayin daga ita sai kura a irin wannan rahoto na kididdiga ci gaban kasashen duniya, dalilin da ya sa kenan shugaban kungiyar matasa ta MOJEN, Siraji Issa ke murnar sabon matsayin da bankin duniya ya saka kasar akansa a bana.

To sai dai ra’ayoyi sun sha bamban a game da wannan batu domin shugaban kungiyar Voix des Voix wato muryar talaka, Nassirou Saidou na cewa yanayin rayuwar jama’a shi ne ma’auni mafi inganci wajen tantance mizanin ci gaban kowace kasa.

A shekarar 2014 bankin duniya ya bayyana cewa kashi 45.4 daga cikin 100 na jama’ar Nijer kusan million 20 ne ke rayuwa cikin yanayi na matsanancin talauci.