Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar HALCIA Ta Jamhuriyar Nijar Ta Kwato Sama Da Cfa Miliyan 2000


Kudin CFA
Kudin CFA

Hukumar yaki da cin hanci ta Jamhuriyar Nijar, ta bada sanarwar karbo makudan kudaden haraji da suka makalle a hannun wasu kamfanoni da ‘yan kasuwar kasar da wadanda aka yi rubda ciki akansu a maimakon a zuba a asusun gwamnati.

Sama da million 2000 na cfa ne hukumar ta HALCIA tace ta yi nasarar karbowa daga hannun wadanda suka yi mursisi akan kudaden harajin fiton kaya da makamatansu.

A hirar shi da manema labarai, shugaban sashen kula da bincike a hukumar yaki da cin hanci Capitaine Sama’ila Elhadji Issouhou ya bayyana cewa, binciken ya shafi kudaden haraji da kuma wadansu kudaden da ba na haraji ba da ya kamata a sa a asusun gwamnati amma aka yi rubda ciki da shi.

HALCIA - Nijar
HALCIA - Nijar

Hukumar ta yabawa takwarorinta na wasu kasashen yammacin Afrika saboda gudunmuwar da suka bayar wajen gudanar da wannan bincike da ya shafi abubuwan da suka wakana a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

A nashi bayanin, kwamishina Ibrahim Alio Sanda ya ce kasashen da suke ba su hadin kai da goyon baya sun hada da Benin, Togo, da Burkinafaso,

Yanzu haka wasu jami’an hukumar HALCIA sun kaddamar da bincike ba sani ba sabo a wasu daga cikin ma’aiikatun ministoci a kalla 8 da nufin tantance wainar da aka toya a tsawon wasu shekaru a ci gaba da farafutar mahandama dukiyar kasa inji darektan yada labaranta Moutari Attaou.

Hukumar HALCIA Ta Kaddamar Da Shirin Bada Takaddun Shiga Kasashen ECOWAS
Hukumar HALCIA Ta Kaddamar Da Shirin Bada Takaddun Shiga Kasashen ECOWAS

Baya ga batun kwato kudade daga hannun masu kewayewa hanyoyin biyan haraji da hadin kan wasu baragurbin ma’aikata da wadanda ke karkata akalar dukiyar kasa, hukumar HALCIA ta sha alwashin ci gaba da bin diddigi don ganin an gurfanar da su a gaban koliya.

hukumar-halcia-mai-yaki-da-cin-hanci-a-nijer-ta-tashi-haikan-kan-batun-haraji

hukumar-yaki-da-cin-hanci-ta-nijer-ta-kudiri-aniyar-sa-ido-a-zaben-kasar

hukumar-yaki-da-cin-hanci-a-jamhuriyar-nijer-ta-kara-kaimi

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Hukumar HALCIA Ta Jamhuriyar Nijar Ta Kwato Sama Da Cfa Miliyan 2000-2:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG