A wata sanarwar da suka fitar da yammacin ranar Alhamis a karkashin jagorancin shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Batonnier Me Boubacar Oumarou, lauyoyin sun fara ne da nuna rashin jin dadinsu a game da abinda suka kira tauye ’yancin aikin lauya, matsalar da ke kokarin samun gindin zama a yanzu haka a Nijer, bisa la’akari da yadda kungiyar lauyoyi ta Barreaux de l’ordre des Avocats ke samun korafe-korafen lauyoyin da ke zargin an hana masu samun sukunin kare mutanensu da aka garkame a kurkuku bayan tarzomar watsi da sakamakon zabe, yayin da suka ce matakin kulle irin wadannan mutane a gidan kaso da ke nesa da alkalin da ya kama su abu ne da ya sabawa yunkurin kusantar da jama’a da mashara’anta.
Lura da yadda cece-ku-ce ke kara tsananta a tsakanin bangarorin siyasa a kowacce safiya tun bayan fitar da sakamakon zaben 21 ga watan Fabarairu, ya sa kungiyar Barreau de l’ordre des Avocats jan hankalin ‘yan siyasa su gujewa bin son zuciya.
A tasa sanarwar da ya bayar a daren jiya ta kafar labarai mallakar gwamnati, alkali mai kare muradan hukuma a kotun birnin Yamai ya bayyana cewa ya zuwa ranar 11 ga watan Maris mutane 652 suka shiga hannun ‘yan sandan farin kaya sanadiyar zanga-zangar da aka yi fama da ita a birnin Yamai, cikinsu har da yara kanana kimanin 160 wadanda kuma aka damka 135 a hannun iyayensu. Daga cikin wadanda suka manyanta an wanke 183 yayin da ake tuhumar mutun 328 da aikata laifi daga 1 zuwa abinda ya zarce haka.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma