Bangarorin PDP Biyu Sun Yi Gangami a Yola Jihar Adamawa

Bayan ficewar wasu gwamnoni daga jam'iyyar PDP ana zaton jam'iyyar bata da wani bangare kuma. To amma ba haka abun yake ba a jihar Adamawa inda bangarorin biyu suka yi gangami.
A wani taron gangami na kwato jam'iyyar PDP da aka yi a Yola jihar Adamawa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta bakin mai bashi shawara kan harkokin siyasa Ahmed Ali Gulag ya ce ba zasu kyale ba wasu su ci amanar jam'iyyar.

Yace kafin zabe mai zuwa zasu fitar da duk 'yan tawaye daga jam'iyyar. A wurin gangamin wadanda suka yi jawabi sun hada da 'yan bangaren Bamanga Tukur da tsohuwar 'yar majalisar dattawa Grace Ben da Sanata Bello Tukur da Idi Hong da Mr. Boni Haruna tsohon gwamnan Adamawa. Dukansu sun yi istifakin cewa Jonathan zasu sake tsayarwa a zabe mai zuwa na shekarar 2015.

Yayin da 'yan bangaren Bamanga Tukur ke yin taron daya bangaren jam'iyyar a karkashin shugabancin Alhaji Umaru Mijinyawa Kugama su ma sun gudanar da nasu taron inda suka gayyaci shugabannin kananan hukumomi ashirin da daya da kuma 'yan majalisar dokokin jihar Adamawan. Mr. P. P. Elesha sakataren bangaren Kugama ya ce PDP ta jihar Adamawa tana karkashin Mijinyawa Kugama domin shi ne aka zaba sai dai bangaren Bamanga Tukur su cigaba da yin fitina.

Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Bangarorin PDP Biyu Sun Yi Gangami Yola Jihar Adamawa - 1:27