Ban Ki-Moon Ya Yabawa Shugaban Kasar Mali Kan Matakan Da Yake Dauka

Mali

Majalisar Dinkin Duniya za ta tura karin dakaru a cigaba da tallafawa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a Mali, a cewar Majalisar, yayin da ake bikin cika shekara guda da shiga tsakanin da ta yi a rikicin kasar da ke Yammacin Afrika.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, babban sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon, ya yaba da irin matakan da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubakar Keita ya ke dauka.

Ya kuma yi fatan za a kara himmatuwa wajen aiwatar da shirin da aka cimma, lura da cewa akwai kalubale da dama a gaba.

A makon da ya gabata, Firai minister Modibbo Keita ya gabatar da wani jawabi a gaban kwamitin sulhu na Majalisar a birnin New York, inda ya maida hankali kan batun karin dakaru 2,500 da za a tura domin tallafawa sojoji dubu 12,000 da ke kasar a yanzu.

Sai dai ya yi gargadin cewa samar da maslaha kan rikicin na Mali ba wai ya ta’allaka bane kawai akan yawan dakarun da aka tura.

Ya ce “mafitar ba wai ta ta’allaka ne da yawan dakaru ba, a’a, sai dai inganci.” A cewar Mr Keita a wata hira da ya yi da sashen Faransanci na Muryar Amurka.

Ya kuma yiwa kwamitin sulhun tuni game da batun karfafa rundunar hadin gwiwa ta MINUSMA wacce aka kafata a shekarar 2013 da zimmar wanzar da zaman lafiya a kasar, tun bayan da ‘yan tawayen Abzinawa suka yi bore a shekarar 2012.