Bamu Yarda Da Karin Farashin Man Fetur Ba - Marasa Rinjaye A Majalisar Wakilai

Kwamitin kolin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki tare da janye abinda ya kira da karin farashin man fetur 'maras dalili'.

Kwamitin kolin marasa rinjaye a majalisar wakilan Najeriya ya yi tir da sanarwar baya-bayan nan da kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL) ya yi ta kara farashin man fetur.

A sanarwar da Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar, Kingsley Chinda, ya fitar yau Alhamis, ta ruwaito kwamitin kolin marasa rinjaye na cewa, bawai kawai lamarin yazo ne a lokacin da bai dace ba, a’a karin yin burus ne da irin mummunan halin matsin tattalin arzikin da al’umma ke fama da shi ne a fadin Najeriya.

Kwamitin kolin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki tare da janye abinda ya kira da karin farashin man fetur 'maras dalili'.

Sanarwar ta kara da cewa, “a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin tattalin arzikin da ba a taba gani ba, da suka hada da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da rashin ayyukan yi da faduwar darajar naira, karin farashin man fetur ba zai yi komai ba illa kara ta’azzara muwayacin halin da talakan Najeriya ke ciki”.

A Talatar da ta gabata ne kamfanin man NNPCL ya kara farashin litar man fetur daga naira 568 zuwa naira 855 ko 897 (ya danganta da nisan wuri), duk kuwa da matsalar karancin man da ta jima tana addabar Najeriya.

Ku Duba Wannan Ma NNPC Ya Kara Farashin Litar Mai A Najeriya - Rahotanni
Ku Duba Wannan Ma Kanfanin Mai Na Najeriya NNPC Na Fuskantar Matsalolin Kudi

Sabon karin farashin fetur din na zuwa ne bayan da kamfanin NNPCL ya amince da cewar masu sayar masa da man na bin sa bashin daya haura dala bilyan 6.