Cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar ta MAN Segun Ajayi-Kadir ya fitar a ranar Laraba ta ce matakin zai iya shafar kudaden shigar jama’a.
Ajayi-Kadir na mayar da martani ne kan karin farashin man fetur da aka yi a kasar a ranar Talata.
Kamfanin NNPC ya kara farashin litar mai daga naira 568 zuwa naira 855, matakin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a sassan Najeriya wacce ta dogara da mai a matsayin babbar hanyar samun kudaden shigarta.
“Yayin da farashin mai ya tashi, kudaden da mutane ke kashewa zai karu a fannonin sufuri da makamashi, wanda hakan zai rage kudaden da suke samu.” Ajayi-Kadir ya ce a cikin sanarwar kamar yadda rahotanni suka nuna.
Ya kara da cewa lamarin zai fi shafar kananan masana’antu saboda kudaden da suke juya wa ba su taka kara sun karya ba.
Ko da yake, Shugaban na MAN ya ce bai yi mamaki da karin kudin litar man ba, duba da cewa farashin mai ya tashi a kasuwar duniya.
“Farashin mai ya tashi a duniya. Matatun manmu ba sa aiki kuma muna shigo da mai ne.” Ajayi-Kadir ya kara da cewa.
Dandalin Mu Tattauna