Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Rahotan Baiwa Kamfanin NNPCL Umarnin Kara Farashin Man Fetur


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ce ta umarci kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sayar da litar man akan naira dubu daya.

Sanarwar da mashawarci na musamman a kan harkokin yada labarai ga Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, Nnemaka Okafor ya fitar, a yau Talata tace, an kitsa rahoton ne da nufin haddasa fitina da rudani a bangaren albarkatun man fetur din kasar.

Rahoton ya yi ikirarin cewa Lokpobiri ne ya baiwa kamfanin NNPCL umarnin.

Sai dai Ministan ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta taba yiwa NNPCL katsalanda a kan farashin man fetur ba.

“Ma’aikatar albarkatun man fetur ba ta yi kuma ba za ta taba yin katsalandan shawarwarin cikin gida da NNPCL ya yanke ba, ciki har da batun farashi. Dukkanin wani hasashe da ya saba hakan ba wai kawai kuskure ba ne, ya ma bayyana rashin fahimta game da yanayin cefanar da bangaren albarkatun man fetur din Najeriya.

“Muna masu yin allawadai da wadannan zarge-zarge a matsayin marasa tushe kuma masu mummunar manufa sannan wani yunkuri ne na tunzara al’umma. Muna kalubalantar duk wanda yake da wata shaida; rubutacciya ko nadaddiyar murya ko faifan bidiyo game da wadannan zarge-zarge da ya fito ya bayyanasu.”

An ruwaito sanarwar na cewa, “ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya ta fito ta fayyace karerayin da ake yadawa a kafafen sada zumunta, dake ikirarin cewar Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya umarci kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya kara farashin man fetur sama da yadda aka amince dashi a hukumance.”

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG