Bama bamai su tashi a Nigeria

Jami'an kiwon lafiya ke kula da wani, wanda tashin bam a Madalla kusa da Abuja ya jikata.

Wani bam ya tashi a wani coci a kusa da Abuja baban birnin taraiyar Nigeria a yayinda mabiyar addini Kirista ke bikin Kirisimeti a yau Lahadi harma an kashe akalla mutane goma sha biyar.

Wani bam ya tashi a wani coci a kusa da Abuja baban birnin taraiyar Nigeria a yayinda mabiyar addini Kirista ke bikin Kirisimeti a yau Lahadi harma an kashe akalla mutane goma sha biyar.

Daga bisani an bada rahoto tashin wani bam kusa da wani coci a birni Jos. Ba’a dai tantance nan da nan ko an auna cocin bane kuma ba’a samu rahoton ko wasu sun jikatta ba

Tashin bam na kusa da birnin Abuja ya faru ne a lokacinda Kiristoci ke cikin cocin Saint Theresa a Madalla. Jami’an ceto sun bada rahoto cewa sun kwashe gawarwarki goma sha biyar amma sunyi kashedin cewa kila yawan wadanda suka mutu su karu.

Shedun gani da ido sunce akwai zaman dar dari bayan tashin bama baman a yayinda wasu matasa da suka fusata sun ka sa shingayen da suka cinawa wuta, su kuma yan san sai suka yi harbi cikin iska domin tarwatsa mutane.

Babu dai wata kungiyar data yi ikirarin tashin bama baman.

Wannan al’amari ya faru ne a yayinda hukumomi suka ce tarzoma a ciki da kewayen biranen Maiduguri da Damaturu a arewa masu gabashin kasar su kashe akalla mutane sittin da takwas cikin yan kwanakin da suka shige.

Aika Sharhinka