Kwamitin da gwamnatin jihar Nija ta kafa domin ya binciki yawan barnar rayuka da dukiyoyin jama'a da aka yi sakamakon harin bam da aka kai kan wata coci a garin Madalla,ranar kirsimeti cikin jihar, ya mika rahotonsa.
Da yake magana da wakilin Sashen Hausa na Muriryar Amurka a Minna, shugaban kwamitin, wanda har ila yau shine kwamishinan ma'aikatar kananan hukumomi Alhaji Yusuf Garba Tagwai yace mutane 38, wasu 80 ne suka jikkata a harin.
Ya kara d a cewa gidaje 36,motoci bakwai, da babura hudu ne aka lalata sakamakon harin da aka kai ranar lahadi da ta wuce.
Sauri: