Bam Ya Hallaka Mutane Uku A Wani Gangamin Siyasa

Wani taron jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya. Akan auna tarurrukan siyasa da bama-bamai a Nijeriya a 'yan kwanakin nan.

‘Yan sanda a yankin tsakiyar Nijeriya sun ce wani bam ya tashi a wurin wani gangamin siyasar da jama’iyya mai mulki ta shirya, ya hallaka mutane uku ya kuma raunata 21.

‘Yan sanda a yankin tsakiyar Nijeriya sun ce wani bam ya tashi a wurin wani gangamin siyasar da jama’iyya mai mulki ta shirya, ya hallaka mutane uku ya kuma raunata 21.

Harin ya auku ne a yau Alhamis a garin Suleja, da ke jahar Naija, da ke arewacin Abuja, babban birnin kasar.

Kakakin hukumar ‘yan sanda Olusola Amore y ace maharan sun jeho bam din ne daga wata motar da ke gudu. Y ace bam din ya tarwatse ne a inda mata ke saida abinci ga wadanda su ka zo gangamin da jam’iyya mai mulki, PDP ta shirya.

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar ta PDP, Babangida Aliyu, ya halarci gangamin. Jami’ai sun ce bai sami rauni ba a wannan harin.

Babu dai wanda ya dau alhakin kai harin kuma ba a kama kowa ba tukunna.

Za a gudanar da zaben Shugaban kasa da na ‘yan Majalisa da na matakan jiha a wata mai zuwa a Nijeriya. Ana samin karin tashe-tashen hankula a sa’ilinda lokacin zaben ke kusatowa.