Rundunar ‘yansanda ta jihar Flato ta yi kira ga al’uma su kwantarda hankalinsu dangane da kama wata mota daka dauke sinadaran hada boma-bomai da nakiyoyi,tana mai cewa kayan na farar hula ne.
Cikin hira da wakiliyar Sashen Hausa a Jos,fadar jihar Flato, babban jami’in kula da sashen boma-bomai na rundunonin ‘Yansanda dake Plateau da Bauci, ASP Ebel Nbiba yace kayan mallakar wani kamfani ne da ake kira Duwan,dake aikin gine ginen hanyoyi da wasu ayyukan raya kasa.
Da yake amsa wata tambaya,ASPEbel yace bincike da suka yi ya nuna cewa babu wani lokaci da aka karkata irin wadan nan sindaran daga kamfanin domin wani aikin barna, ko halaka mutane.
Ranar Jumma’a ce rundunar wanzarda zaman lafiya cikin jihar, ta kama motar a wani wurin duba motoci.
Ana ci gaba da tsare matukin motar da ‘Dansanda dake bashi kariya.