Babban jami’in dake Magana da yawun hukumar zaben Nigeria Nick Dazan, yace a yau laraba hukumar zata rarrabawa dukkan jam’iyyun siyasar Nigeria takardun dake dauke da jerin sunayen wadanda suka cancanci kada kuri’a kuma suka yi rajista domin zaben watan Afrilu mai zuwa.
Hukumar zaben Nigeria tace yanzu kam ta tabbatar da sahihancin jerin sunayen wadanda aka yiwa rajistar, bayan jami’anta sun nazarci jerin sunayen wadanda suka yi rajistar aka kuma fidda baragurbi da wadanda suka yi rajista fiye da daya.Kusan ‘yan Nigeria miliyan sittin da takwas ne suka cancanci kada kuri’a.
A wani bangaren kuma,’Yan sandan Nigeria suna tsare da wani Shehin Malamin Islama tare da masu wa’azin dake tare dashi su hudu saboda zargin aikata laifin yin batunci ga takardun hotunan dake tallan manufofin shugaban Nigeria Goodluck Jonathan. ‘Yan sandan sun kame Sheikh Abubakar Jibril da sauran wadanda ake zargi dake tare da shi ran litinin a garin Sokoto. Sai dai shugabannin addini a Sokoto, da Musulmi keda rinjaye, sun yi zargin cewa kama Shehin Malami nada nasaba da wata manufa ta siyasa.