Bakin Haure Amurkawa Zasu Yi Babban Tasiri A Zaben 2024

Nevada Elections Asian Americans

Batun bakin haure ya kasance batu mai mahimmanci a zaben shugaban kasar Amurka na 2024, inda kaso 28% na Amurkawa suka bayyana shi a matsayin babbar matsala a kasar.

Amurkawan da suka cancanci kada kuri’a a zaben 2024 sun kunshi kaso daya cikin goma na bakin hauren da suka zama ‘yan kasa.

Batun bakin haure ya kasance batu mai mahimmanci a zaben shugaban kasar Amurka na 2024, inda kaso 28% na Amurkawa suka bayyana shi a matsayin babbar matsala a kasar. Duk da haka, wannan damuwar da ake dada nunawa na zuwa a wani lokaci ne da alkaluman bakin hauren da suka cancanci kada kuri’a ya karu.

A shekarar 2022, alkaluman bakin haure da ke Amurka sun kai miliyan 46,000,000, wato kaso 14% cikin dari na jumlar al’ummar Amurka baki daya, alkaluma mafi girma tun bayan shekarar alib -dar-tara-da-ashirin (1920).

Cibiyar bincike ta Pew ta yi kiyasin akalla mutum miliyan 23,000,000 da suka cancanci kada kuri’a bakin haure ne da suka zama ‘yan kasa, alkaluman da suka kai su ga zama kaso daya cikin goma na Amurkawa da suka cancanci kada kuri’a a kasar.

Baya ga batun habbakan alkaluman bakin haure, alkaluman binciken Pew sun nuna yawan bakin hauren da ke neman damar zama ‘yan kasa sun karu sakamakon wani shiri da gwamnatin Biden ya kirkiro don saukaka tsarin zama dan kasa.

Ba abin mamaki bane ganin yadda alkaluman bakin hauren da suka zama 'yan kasa a Amurka suka fi yawa a jihohi mafi yawan al'umma guda 4 a kasar, wato jihar California, New York, Florida da Texas, inda sama da rabin wannan rukunin Amurkawan da suka cancanci kada kuri'a suke.