Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da tsohon Shugaban kasa Donald Trump sun yi tsokaci kan yadda ya kamata a kula da mata a cikin al’umma yayin da suke neman kuri’u a ranar Alhamis a jihohin Arizona da Nevada, jihohin biyu na kudu maso yammaci kasar da ake fafatawa a fagen siyasa.
Harris kenan take fadawa mata cewa, “Idan na zama shugabar kasa, na muku alkawarin zan samar da maslaha kan matsaolin da kuke fuskanta.”
Yayin da yake nasa gangamin yakin neman zaben Trump ya ce:
“Ta ce zan soke tsarin kiwon lafiya na medicare da kudaden ritayar ma’aikata, ai kun san cewa karya take yi. Asali cikin shekaru hudu na kara karfafa su ne.”
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna Harris, ‘yar takarar jam’iyyar Democrat da kuma Donald Trump na jam’iyyar Republican, sun yi kunnen doki a jihohin biyu.
Arizona da Nevada na daga cikin jihohin bakwai da ake fafatawa sosai a fadin jojihohin 50 na kasar da mai yiwuwa su tantance sakamakon zaben kasa da za’a yi a ranar Talata mai zuwa.
A sauran jihohi 43, kuri’ar jin ra’yoyin jama’a da aka gudanar sun nuna cewa Trump ko kuma Harris ko dai sun yi wa juna fintinkau ko kuma sun ba da tazara mai yawa.
Neman masu kada kuri’a ‘yan Latino ya zama shi ne babban batun na yakin neman zaben a jihohin Arizona da Nevada.
Trump ya lashe Arizona a zaben shugaban kasa da aka yi a 2016 amma ya rasa jihar ga shugaba Joe Biden a 2020. Jam’iyyar Democrat ta lashen Nevada a zabukan biyu.
Dandalin Mu Tattauna