Bakin Haure 27 Sun Mutu A Gabar Tekun Tunisiya

Har yanzu ana ci gaba da neman fasinjojin daka iya bata, a cewar hukumar tsaron kasar Tunisia, wacce ke kula da gabar ruwan kasar.

Bakin haure 27, ciki harda mata da kananan yara sun mutu sakamakon kifewar wasu kwale-kwale 2 daura da yankin tsakiyar Tunisia, sannan an ceto wasu mutane 83, kamar yadda wani jami'in hukumar tsaron farin kaya ya shaidawa kamfanin dillancin labaran afp a yau Alhamis.

Fasinjojin da aka ceto da wadanda suka mutun, da aka tsinta a kusa da tsibirin Kerkenneh dake daura da lardin tsakiyar Tunisia, nada niyar isa turai kuma dukkaninsu sun fito ne daga kasashen kudu da saharar Afrika, kamar yadda shugaban hukumar tsaron farin kaya ta Tunisia, Zied Sdiri ya bayyana a birnin Sfax.

Har yanzu ana ci gaba da neman fasinjojin daka iya bata, a cewar hukumar tsaron kasar Tunisia, wacce ke kula da gabar ruwan kasar.

Tunda fari a ranar 12 ga watan Disemban daya gabata, hukumar tsaron gabar tekun ta ceto bakin hauren Afrika 27 a kusa da garin Jebeniana, dake arewacin Sfax, saidai an bada rahoton mutuwa ko batan mutane 15.

Tun farkon shekarar data gabata, hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Tunisia ftdes ta kirga tsakanin bakin haure 600 da 700 da kodai suka mutu ko suka bata sakamakon hatsarin kwale-kwale a gabar tekun Tunisia.

Fiye da bakin haure 1, 300 sun mutu ko sun bata a 2023.