Da yake jawabi a jiya Litinin a yayin wani taron karawa juna sani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shiryawa kwamishinonin shari’a na jihohin Najeriya, Fagbemi yace zai bada shawara a taron gyaran kundin tsarin mulki na gaba cewar bai kamata duk wadanda aka taba samu da laifin cin hanci da rashawa su ci gajiyar alfarmar yafiya da afuwa ta gwamnati ba.
A cewar antoni janar na tarayyar, “zan bada shawara a taron gyaran kundin tsarin mulkinmu na gaba cewa a tsame wadanda aka samu da laifin cin almundahana daga cin gajiyar alfarmar yafiya da afuwar gwamnati”
Ya kuma jaddada mahimmancin hadin kai tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki, musamman masu rike da mukamin antoni janar, a yakin da ake yi da almundahana, inda ya bukace su da kada su bari kabilanci da bita da kullin siyasa da hamayya da bambancin addini suyi tasiri a ayyukansu.
Fagbemi ya kuma bukaci hukumomin yaki da almundahana dasu tabbatar sun gudanar da cikakken bincike akan zarge-zargen cin hanci da rashawa gabanin su gurfanar da wadanda ake zargi gaban kuliya domin kaucewa kace-nace a kafafen yada labarai.