Tsarin sauya sheka a Najeriya dai ya samu karbuwa. Sai dai Kwamrad Daniel Likam wanda shine shugaban yan kudancin jihar Taraba, ya bayyana yadda yan siyasa manya da kanana ke barin jam’iyunsu ta asali zuwa wata, mussaman wacce ke rike da mulki, wasu na yin hakan ne don a cigaba da damawa da su wasu ko don su boye kazantar da ke jikinsu na rashawa, ya bada misali da jiharsa, inda senatan su na southern Taraba, Sanata Emmanuel Bwacha ya koma APC bayan shekaru kusan 8, babu abun a-zo-a-gani.
Toh sai dai a martanin da ya bayar Sanata Emmanuel Bwacha da ake zargi da canja sheka saboda neman kariya daga ayyukan rashawa dake tattare da shi ya wanke kansa in da ya ce ba shi da wani kariya saboda a kowani lokaci hukumar EFCC za su iya bincikensa. Ya kuma ce barinsa PDP zuwa APC ba don wani abu ba ne ila don an nuna masa ba a son sa a PDP ne.
Ku Duba Wannan Ma Jam’iyyar PDP Ta Zargi Gwamnatin APC Da Rashin Kawar Da Matsalar Tsaro A NajeriyaToh ko mai doka ke cewa game da wannan batu, kwararen lauya a Najeriya Barista Shitu Muhammad ya yi kari da cewa sashin 68 na constitution bai ba dama canza sheka ba idan jam’iyyar sun sami rabuwar kai ba ko kuma ana son a samu maja.
Duk da cewa wannan gwamnati karkashin jagoranci shugaba muhammadu Buhari ta yi alkwarin hukunta duk wani da bincike ya gano na dauke da laifin cin hanci da rashawa kowanne shi kuwa, Ambasada Ali barakat shugaban Amintattu na kungiyar Buhari Youth Organisation ya yi kira ga gwamnati data kara kaimi wajen bincike kan zargin badakalar gwamnatin jihar zamfara ta da shude.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5