Wata kungiya mai maradun dawo da sarkin Kano Sanusi na biyu ce ta fara mika wasika zauren Majalisar kimanin makonni uku da suka gabata ta neman Majalisar ta rushe masarautu hudu da gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro kusan shekaru biyar da suka shude.
Daga bisani aka rinka samun kwararar wasiku daga sassan sabbin masarautun suna jaddada goyon bayan su ga ci gaba da wanzuwar masarautun tare da jan hankalin ‘yan Majalisar dokokin ta Kano kan hadarin dake tattare da rusa masarautun da kuma dawo da Sanusi karagar Mulki.
Ko da yake Majalisar dokokin ta Kano bata kai ga fara mahawara ko tattaunawa ba akan wannan batu ba, Shugaban masu rinjaye na Majalisar Hon Lawan Hussaini ya yi karin haske dangane da halin da ake ciki inda ya bayyana cewa, “Idan policy wato manufar gwamnati ya yi dai dai da abin da mutane suke kawo mana to za mu gaggauta aiki da irin bukatu ko sha’awarta, mu muna saurarorin sha’awar gwamnatin mu ta karkashin jam’iyyar mu ta NNPP ne”.
To amma masana dake sharhi kan lamuran Jama’a, sun fara tsokaci tare da bada shawarwari ga gwamnati da Majalisar dokokin ta Kano game da hanyoyin da su ka kamata su bi wajen warware wannan takaddama cikin lumana.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, masanin kimiyyar siyasa da harkokin Mulki dake koyar da wannan fanni a Jami’ar Bayero, Kano na cewa, “Kamata ya yi su gudanar da kuri’ar raba gardama ko ra’ayin Jama’a, sahihiya, wadda a turanci ake kira “referendum”, wadda a tsarin musulinci akwai ta, a tsarin demokaradiyya akwai ta kuma hakan ita ce hanya sahihiya da za’a kaucewa, fuskantar barazanar tsaro game da lamarin”.
Yayin da wasu mutane ke amfani da kungiyoyi wajen matsawa gwamnati da Majalisar dokoki lamba kan bukatar ci gaba da wanzuwar masarautu biyar a jihar Kano ko kuma a rusa 4 a bar daya, babban burin galibin al’ummar jihar shine gwamnati ta magance halin matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5