A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Hassan Turaki wanda ya shafe sama da shakaru saba’in (70) yana rayuwa a karamar hukumar Yola ta Arewa kuma daya daga cikin daddawan da suka kai wannan korafin zuwa Majalisar Dokokin jihar, ya ce su ba karin masarautun gargajiya suke bukata ba domin kuwa wadanda suke aiki a karkashin hakiman ma sun shafe sama da watanni tara zuwa goma basu da albashi sannan a ce za a kara wasu , ya ce su basu amince da wannan batun ba.
Shugaban masu rinjaye na Majalisa jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin kirkiro da sabbin gundumomi (Hakimai) a jihar Adamawa, Hamman Tukur Yetisuri kuma memba mai wakiltar-Jada Mbulo a Majalisar Donkokin jihar Adamawa ya ce wannan korafi da alumman jihar suka kawo haka za su dauka sukai gaban Majalisar don a dubi lamarin.
Da ya ke tsokaci a kan lamarn, Dr Mahadi Abba malami a jami’ar Modibbo Adamawa dake Yola kuma masanin al’amuran yau da kullum cewa ya yi Majalisar Dokokin jihar basu yi abinda ya yakamata ba saboda ba aji ra’ayin alumman jihar ba, saboda haka a duba lamarin kuma ayi shi ta hanyar da ya dace.
Saurari rahoto cikin sauti daga Salisu Muhammed Garba: