Duk da cewa kungiyiyoyin kwadago ta Najeriya wato NLC da TUC sun rufe hedikwatar hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya wato NERC da ofishin kamfanonin rarraba wutan lantarki na DisCos a sassan kasar daban-daban, wasu ‘yan Najeriya sun ce zanga-zangar bai yi wani tasiri ba sakamakon yadda ‘yan kasar suka ci gaba da gudanar da harkokin su yadda suka saba.
‘Yan Najeriya daga shiyoyin kasar kama daga Kano, Filato, Bauchi, Kaduna, Neja da dai sauransu sun ce lallai kungiyoyin sun rufe ofisoshin DisCos amma ba su ga wani tasiri da zanga-zangar ya yi a kasar ba.
Saidai sakataren tsare-tsaren kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya ce zanga-zangar lumanar da suka gudanar ya yi tasiri matuka sakamakon yadda suka aika sakonninsu ga gwamnati.
Mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum kuma shugaban kamfanin kasuwanci da zuba jari na GITC, Mal. Baba Yusuf, ya ce tasirin da kungiyoyin NLC da TUC ke yi ya ragu kwarai da gaske sakamakon yadda ake zargin suna hada kai da gwamnati a bayan fagge a sanya talaka cikin wani yanayi.
Idan ana iya tunawa, gwamnati ta sanar da janye tallafin da gwamnatin tarayya ke baiwa bangaren wutar lantarki da karin kudin wutar lantarki na Band A ne a farko-farkon watan Afrilun lamarin da kungiyoyin kwadagon suka nuna rashin goyon bayan su a ka har ya kai ga fara zanga-zangar na yau a fadin kasar.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf:
Your browser doesn’t support HTML5