Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta musanta zargin da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka yi cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa, tare da taimakon jami’an tsaro na ƙketare, ciki har da na Najeriya, suna da hannu a harin da aka kai kan bututun mai na Nijar-Benin.
A ranar 13 ga Disamba, 2024, a Gaya, yankin Dosso na Jamhuriyar Nijar aka kai hari kan bututan man na Nijar.
“Gwamnatin Najeriya tana mika ta’aziyyarta ga Gwamnatin Nijar kan wannan mummunan hari da aka kai kan bututun mai, amma tana bayyana karara cewa wadanda suka aikata harin ba su sami goyon baya ko taimako daga hukumomin Najeriya ba.
“Gwamnatin Najeriya tana da kwarin gwiwa wajen yaki da ta’addanci kuma ba za ta lamunci ko goyi bayan ayyukan irin waɗannan kungiyoyin ba.” Sanarwar ma’aikatar harkokin Najeriya dauke da sa hannun kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ta ce.
Sanarwar ta kara da cewa, “haka nan, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta nuna damuwa sosai tare da bayyana a fili cewa babu sojojin Faransa da ke yankin arewacin kasar da ke shirin kawo cikas ga Gwamnatin Nijar.
“Wadannan zarge-zargen ba su da tushe, kuma ya kamata a watsar da su gaba daya.” Sanarwar ta kara da cewa.
A baya-bayan nan, dangantaka tsaanin Najeriya ta kara kyautatuwa musamman ta fuksar difplomasiyya inda har Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar Paris a farkon watan Disamba.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023 dangantaka ta yi tsami tsakaninta da Faransa.