A baya-bayan nan an yayata cewa, jami’in hukumar INEC ya ce ta yiwu a soke babban zaben da ke tafe ko a dage shi bisa la’akari da kalubalen tsaro.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta bakin Ministan Labarai Lai Muhammed ta bayyana matsayarta da ta sha bamban da abinda a ka yada, inda ta ce ba abinda zai shafi zaben kuma gwamnati ta san hukumar zabe na aiki da jami’an tsaro wajen tabbatar da nasarar zaben.
A wajen wani taron horar da jami’an hukumar zaben a shelkwatar INEC da ke Abuja don zuwa sassan kasa su wayar da kan sauran jami’an zabe, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya ce ba wani sauyi game da ranakun zaben.
Ya kara da cewa hare-hare kan wasu ofisoshin hukumar da aka kai a baya-bayan nan ne su ka jawo kalaman don jan hankalin rundunonin tsaro su yi tsayin daka don magance matsalar gabanin zaben.
Da ta ke karin bayani kan halin da a ke ciki, jami’a a sashen labarai a hukumar INEC Zainab Aminu, ta ce hankalin ‘yan takara da masu kada kuri’a ya kwanta don ba wani sauyi kan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu. Sai kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris.
Zainab Aminu ta kara da cewa, jami’an tsaro sun ba hukumar tabbacin cewa ba wani fargaba ga shirin zaben don haka kowa ya shirya don kada kuri’arsa.
Gabanin bullar wannan labarin INEC ta sanar cewa an kai hari kan ofisoshinta a kimanin jihohi 10 da ke kudancin kasar, musamman a kudu maso gabas inda ‘yan tawayen Biafra ke neman yin kafar angulu a harkar zaben don bunkasa muradansu na ballewa daga Najeriya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5