SOKOTO, NIGERIA - An jima ana tafka rikicin cikin gida a jam'iyar PDP mai adawa a Najeriya a jihar Zamfara inda can ma ita ce babbar jam'iyar adawa.
Rikicin dai wanda ya yi sanadin gudanar da zabubukan fitar da ‘dan takarar gwamna har sau biyu tsakanin Dauda Lawan Dare da Ibrahim Shehu Gusau, yau kotun daukaka kara dake zama a Sakkwato ta kawo karshensa inda ta tabbatar da cewa Dauda Lawan Dare shine halataccen ‘dan takara na jam'iyar.
Bayan da kotun ta yanke hukunci daya daga cikin lauyoyin Dauda Lawan Dare ne, Shehu Ajiya ya yi mana tsokaci akan hukumcin da ta yanke.
Ya ce kotun ta yi bayani dalla-dalla akan korafin da masu shigar da kara ke yi kuma ta yanke hukunci bisa doka inda ta baiwa Dauda Lawan Dare takarar gwamna a jam'iyar ta PDP.
Kokarin jin ta bakin bangaren na lauyoyin da ke tsayawa Ibrahim Shehu sai dai sun yi batan dabo bayan yanke hukuncin domin mun neme su mun rasa.
Mukaddashin shugaban jam'iyar PDP a jihar ta Zamfara Mukhtar Ahmad Lugga wanda ya halarci zaman kotun shi ma ya yi tsokaci akan wannan galaba da jam’iyar ta samu.
Ya ce nasara ce ga dukkan talakan jihar Zamfara kuma nasara ga tsarin dimokradiya. Haka kuma mun yi kokarin neman wadanda zasu yi tsokaci a bangaren Ibrahim Shehu Gusau abin ya ci tura domin wayoyin wadanda muka kira suna kashe.
Da yawa magoya bayan jam'iyar PDP da suka halarci zaman kotun sun nuna jin dadi da wannan hukuncin kamar yadda jami'in yekuwar zabe na Atiku Okowa a Zamfara ya nuna mana.
Yanzu da wannan hukuncin jam'iyar PDP ta dawo tsaf cikin batun takarar gwamna a jihar ta Zamfara a zaben da za'a gudanar wannan shekara.
Saurari rahoto daga Muhammad Nasir: