Babban layin lantarkin Najeriya zai ci gaba da fuskantar barazanar durkushewa saboda gazawar gwamnatin wajen gyara wani muhimmin layin wutar da ke shiyar arewacin kasar sakamakon matsalar rashin tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa.
Wadannan sune kalaman Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, wanda ya bayyana hakan yayin zaman kare kasafin kudin ma’aikatarsa na bana a gaban kwamitin hadin gwiwar majalisar dattawan kasar a kan lantarki.
Adelabu ya yi tsokaci a kan illar lalata layin lantarkin na Shiroro-Kaduna-Mando, wanda ya daina aiki tun bayan lalata shi da aka yi a watan Oktoban 2024.
Wannan gazawar ta kara yin matsin lamba a kan babban layin lantarkin kasar, abin da ke sabbaba yawan durkushewarsa.
“Layin Kaduna-Shiroro-Mando yana daga cikin manyan layukan 2 da ke dakon lantarki zuwa arewacin Najeriya, na 2 shine, layin Ugwuaji-Makurdi, wanda shima an lalata shi sai dai an gyara. Amma layin Shiroro-Kaduna-Mando yana nan a lalace saboda rashin tsaro,” kamar yadda ya bayyana a jiya Litinin.
Ministan ya jaddada cewar yayin da ake sa ran matsalar durkushewar lantarkin ta ci gaba, gwamnati ta mayar da hankali wajen rage yawan faruwarsa tare da ba da tabbacin gyara shi a kan lokaci.