Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kwace $52.88m Da Ake Dangantawa Da Diezani


Za a tura dala miliyan 50 daga cikin kudin da aka kwato zuwa aikin samar da lantarki a karkara ta hannun bankin duniya sannan za a tura ragowar dala miliyan 2 zuwa cibiyar bunkasa harkokin shari’a ta duniya domin fadada tsarin shari’a da yaki da cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Najeriya ta karbi dala miliyan 52.88 daga kadarorin Galactica da aka kwato daga Amurka, wadanda ake dangantawa da tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’ar Najeriya Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan yayin bikin rattaba hannu a kan yarjejeniyar kwato kadarorin tsakanin Najeriya da Amurka a Abuja a yau Juma’a.

Da yake gabatar da jawabinsa Fagbemi ya bayyana cewa za’a tura dala miliyan 50 daga cikin kudin da aka kwato zuwa aikin samar da lantarki a karkara ta hannun bankin duniya sannan za a tura ragowar dala miliyan 2 zuwa cibiyar bunkasa harkokin shari’a ta duniya domin fadada tsarin shari’a da yaki da cin hanci da rashawa.

Fagbemi ya kara da cewa, kwato kadarorin wata babbar nasara ce a cigaba da hadin gwiwar da ake yi tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma dabbaka tsarin gaskiya da adalci.

Shi kuma a nasa jawabin, jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills ya bukaci a sanya idanu tare da sarrafa kadarorin da aka kwato ta yadda za su amfani ‘yan Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG