“Gaskiyar magana itace zamu so ace haka ne labarin yake, kuma matsayin mu shine ba wai maganar bangaren Dogara sun amince da Femi ya zama shugaban masu rinjayen majalisa bane. Matsayin mu shine shugaban masu rinjayen majalisa da mataimakin shugaban masu rinjayen majalisa da mai tsawatarwa, da mataimakin mai tsawatarwa ya zama wajibi a girmama jam’iyya kuma a girmama mafi yawancin mambobin dake wannan majalisar wakilai, wanda sun yarda ga mutanen da za’a baiwa wannan matsayi”
Soba ya kara da cewa “ba matsayi bane na zabe, amma matsayi ne na mutane masu rinjaye in sun ce ga yadda suke so, to ita kanta demokradiyya abunda ta gada kennan. Har yanzu, babu wata matsaya da aka cimma, cewa wadannan mutane shi kakakin majalisa Dogara da mutanenshi sun amince su girmama matsayin jam’iyya kuma su girmama mu, mu da muka fi rinjaye, ‘ya’yan jam’iyyar APC wadanda suka dauki wannan matsayi dai-dai da yadda jam’iyya ta dauka. To mu a samu, a sasanta wannan ce-ce ku ce da ake yi.”
Soba ya cigaba da cewa “ranar Lahadi mun gana da kwamitin gwamnan Sakwatto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. Sauran gwamnonin basu samu zuwa ba amma shi mun zauna tare da shi, kuma mun gaya mishi cewa, yana cikin wannan matasala da majalisa ta fada.”
Injiniya Yunusa Ahmed yana bangaren kakaki Yakubu Dogara ne.
“Ba’a cimma matsaya ba har yanzu, saboda mu dinnan, mun wayi gari yau, tun cikin dare muna ‘meeting’ (ganawa). Mu mun yarda duk da cewa babu wani bin ‘party position’ (umarnin jam’iyya), mun yarda zamu mika gurbin shugaba masu rinjaye zuwa ga magoya bayan Femi Gbajabiamila. Amma da sharadi, sharrudan nan sune a cire arewa maso gabas, domin muna da speaker, a cire kudu maso gabas, don muna da mataimakin kakakin majalisa. Sai a raba wannan gurbi a sauran shiyoyin.
Your browser doesn’t support HTML5