Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yan Jamiyyar APC a Jihar Niger Sunce anyi Musu Ba dai-dai ba


A makon jiya ne dai Gwamna Abubakar Sani Bello ya sauke shugabannin kananan hukumomin da ya gada daga tsohuwar gwamnatin PDP

A yanzu haka dai sauke shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Niger Da Gwamnan yayi tare da maye gurbi su da shugabannin maaikatar kananan hukumomin jihar ya bar baya da kura.

A makon jiya ne dai Gwamna Abubakar Sani Bello ya sauke shugabannin kananan hukumomin da ya gada daga tsohuwar gwamnatin PDP to amma sai ya maye gurbin su da shugabannin maaikatan kananan hukumomin da ake kira DPM a takaice.

To sai dai wasu yayan jamiyyar su ta APC lamarin bai musu dadi ba, domin a cewar su sune yakamata a baiwa rikon kanana hukumomin kafin lokacin zaben .

Alhaji Aminu Bello Kofar Guga tsohon shugaban jamiyyar CPC a yankin gabashin jihar Niger wanda kuma jigo ne a cikin jamiyyar APC a jihar yace gwamna Abubakar Sani Bello ya tafka kuskure.

‘’To a gaskiya duk wanda yake dan siyasa ne wanda ya fara daga kasa wato Grassroot yakai yaji wannan abu da gwamna yayi yasan ba a yi dai-dai ba, ita abinda ke maganar nada kiya teka rage nauyi a shi gwamna abinda bai sani ba domin ko ba kome koda murtum biyar ka nada wadannan ko ba kome wadannan kafin azo lokacin zabe su zasu tallata jamiyyar nan su zasu tallata manufar ka wato Manifestor naka.’’

To amma a nasa gefen tsohon dan majilisar dokokin jihar Niger Ahmed Dogara na jamiyyar ta APC yace sun gamsu da matakin gwamnan.

‘’A state din ba kudi yanzu da yasa maaikatan gwamnati DPM din da yasa ai yace daga zuwa wata ukku za a yi zabe yan siyasan nan da kaga suna korafe-korafen nan basu san ma abinda suke yi bane.’’

A wani taron manema labarai kakakin gwamnan jihar Dr Ibrahim Doba yace sun baiya shugabannin kanana hukumomin ne saboda karancin kudi da suke fama dashi kuma nan da watanni ukku zasu gudanar da zabe .

Tuni dai dattawan jihar Niger suka fara baiwa yan siyasa hankuri.

Alhaji Lawali Shukura shugaban kanfanin shukura Bread na daya daga cikin dattawan.

‘’Sai anyi hakuri abin bana gaggawa bane muna fata jamaa zasu yi hankuri kuma zasu baiwa gwamnati hadin kai zasu taimakawa Gwamnati tun daga ta jiha har zuwa ta tarayya da adduoi na alheri’’.

A daye gefen kuma bayanan sirri na cewa jamiyyar PDP tayi maraba da wannan mataki na gwamnan saboda zai bata damar dibar nata rabon a lokacin gudanar da zaben kanana hukumomin.

Ga dai Mustafa Nasir Batsari da cikakken rahoto

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG