Shugaban kungiyar Muryar Talaka, Zaidu Bala, ya ce su na ta fadakar da matasa game da kaucewa yin magudin zabe.
WASHINGTON, DC —
A daidai lokacin da zaben kasar Najeriya ke kara kusantowa, kuma ganin cewa duk wani rikicin zabe da hannun matasa a ciki saboda galibi da su 'yan siyasa ke yin amfani, Bello Galadanchi ya tattauna da shugaban kungiyar Muryar Talaka, Zaidu Bala Kofa sabuwa Birnin Kebbi, kan irin gudunmowar da kungiyar za ta bayar wajen ganin an yi zabe cikin lumana, da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Zaidu Bala ya kara jaddada cewa kafofin sadarwa na zamani za su yi tasiri sosai a zaben Najeriya na shekarar nan ta 2015 saboda da su matasa ke yin amfani su na fadakar da juna, da mika sakonni, da ma shirya tarurruka tsakanin matasan gari da gari.
Your browser doesn’t support HTML5