Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Yankin Gombi na Farin Cikin Kubutra da Mr. Robert da aka yi


Yayinda al'ummar yankin Gombi ke murnar Kubutar da Mr. Robert da aka yi daga hannun 'yan boko haram, ana kuma ci gaba da maida murtani akan kiran da gwamnan jihar yai na dage zabe mai zuwa.

A watan Yunin shekarar da ta gabata ne ‘yan kungiyar Boko haram suka sace wani dan kasar Jamus Mr. Robert Nitsch Eberhard kusa da masaukinsa da ke cikin garin Gombi a arewacin jihar Adamawa, daga bisani kuma kungiyar ta fidda sanarwar cewa ita ta sace shi.

Yanzu haka dai al’ummar garin Gombi na cike da farin ciki game da kubutar da mutumin da aka yi ranar Talatar da ta wuce. Jama'a da yawa sun shaida cewa garin na cike da farin ciki saboda irin kyawawan halayar Mr. Robert.

Al’ummomin yankin Gombi da sauran wuraren da aka kwato daga hannun ‘yan boko haram a arewacin jihar Adamawa na cigaba da maida murtani game da kiran da gwamnan jihar Mr. Bala John Ngilari yayi na cewa ya kamata a dage batun zaben watan gobe har zuwa watan Afirilu.

Ga dukan alamu dai bana za a sami sauyi a jihohin Adamawa da Taraba ganin yadda jama’a suka zaku da kuma shirya wa zaben.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG