Wannan gargadin ya biyo bayan shirin da Shugaba Jonathan din yayi ne domin ziyarar jihar Borno domin kaddamar da yakin neman zaben sa, kwanaki 10 kenan da shugaba Jonathan din ya ziyarci jihar Borno, inda ya gana da jamiaan soja da sansanin yan gudun hijira dake cikin garin Maiduguri, inda ya jajantawa jamaar jihar.
Wannan gargadin ba zai rasa nasaba da abubuwan da suka faru a jihar Katsina da Bauci ba, inda wasu matasa suka dinga ature ga shugaban kasar, sai dai wannan sanarwan da gwamnan ya rattabawa hannu da mai bashi shawara a harkokin yada labarai Umar isah Gusau ya aikewa manema labarai ta yanar gizo yana cewa ga dukkan bayanan da ya samu wannan ya faru ne a jihohin daba jamiyyar APC ke mulki ba, kuma bai son hakan ya faru, duk ko da suna cewa da nasu bambamce bambance siyasa amma fa duk shugaba shugaba ne a cewar gwamna.
Ko a wancan ziyarar da shugaba Jonathan ya kawo garin Maiduguri sai da wasu matasa suka nuna goyon baya ga wani dan takara na daban, wanda wancan lokacoin ma sai da gwamnan jihar Kashin Shattima yaja hankulan matasar, yana mai cewa a al’adar mu na mutanen arewa muna girmama shugabanni, ina rokon ku duk wanda ke kauna ta da wanda ke son jihar Borno duk wanda ke kaunar zaman lafiya mu bashi goyon baya da darajjar da ALLAH ya bashi, don mulki daga wajen ALLAH ne.
Gwamnan yace dan ALLAH kar a sawo maganar da bata dace ba , sai dai gwamnan yace ba wata sanarwan takaita zirga-zirgan da akayi , sai dai Al’ummar jihar na cike da fargaba domin ganin a waccan ziyarar an takaita zirga-zirga.A inda yan makaranta da yan kasuwa suka wahala sosai.Da aka rufe hanyoyi ba tare da wata sanarwa ba. Wannan yasa wasu yan jihar jan hankulan jamiaan tsaron jihar da babbar muryar cewa suwa ALLAH su taimaka musu suci gaba da gudanar da harkokin su na neman cin abincin su, a cewar wasun su sai sun fita ne zasu samu abinda zasu sa a baka.