Babu Abin Da Zai Samu Kudaden ‘Yan Najeriya - CBN

  • VOA Hausa

Babban bankin Najeriya CBN

Sanarwar da mai rikon mukamin daraktan yada labaran babban bankin, Hakama Ali, ta fitar a yau Talata, ta sake tabbatarwa al’ummar da aniyar bankin ta tabbatar da sahihanci da amincin tsarin hada-hadar kudin Najeriya.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kada su razana, kasancewar ya dauki matakan tabbatar da cewar dukkanin kudaden da suka ajiye a bankunan kasar na cikin aminci.

Sanarwar da mai rikon mukamin daraktan yada labaran babban bankin, Hakama Ali, ta fitar a yau Talata, ta sake tabbatarwa al’ummar da aniyar bankin ta tabbatar da sahihanci da amincin tsarin hada-hadar kudin Najeriya.

Hakan na zuwa ne sakamakon sabuwar hayaniyar da aka tashi da ita a fadin Najeriya a jiya Litinin, dake gargadin abokan huldar wasu bankuna dasu gaggauta debe kudaden ajiyarsu, kasancewar babban bankin kasar (cbn) ya janye lasisin gudanarwar wadannan bankuna.

An ruwaito sanarwar na cewar, cbn baya wasa wajen tabbatar da cewar bankunan na yin biyayya ga ka’idojin da aka shimfida da kyawawan dabi’un da zasu kiyaye mutuncin tsarin hada-hadar kudinmu. a koda yaushe muna auna karfin hada-hadar bankin domin gano ko akwai rauni, hakan na taimakawa wajen tabbatar da cewa bankunanmu sun ci gaba da zama da karfinsu.