Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Kudin Dake Asusun Ajiyar Najeriya Na Ketare Ya Haura Dala Biliyan 37.31 - CBN


Bayanan da aka samu daga babban bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa daga ranar 18 ga watan Satumbar da muke ciki, kudaden ajiyar Najeriya na ketare sun kai mizanin da rabon da aga irin haka tun ranar 4 ga watan Nuwambar 2022, lokacin da suka kai dala biliyan 37.36.

Kudaden dake asusun ajiyar Najeriya na ketare sun kai dala biliyan 37.31, mizanin kimanin watanni 22 rabon daya kai haka, abinda ke alamanta samun karuwar kwararowar kudaden ketare zuwa cikin tattalin arzikin kasar.

Dalilai da dama ne suka taimaka wajen bunkasar asusun ketaren, muhimmai daga cikinsu akwai takardun basussukan gwamnatin tarayya na kudin dala, wadanda ke janyo masu zuba jari daga ketare da kudaden da ‘yan Najeriya dake ketare ke turowa gida da basussukan da gwamnati ke ciyowa hukumomin bada lamuni na duniya da kuma cefanar da hannayen jari da takardun basussuka ga kamfanonin ketare da gwamnatin Najeriya ke yi.

A bisa kididdigar auna irin bunkasar da asusun ya yi tun daga farkon shekara zuwa yau, asusun ajiyar Najeriyar ya karu da kaso 12.99 cikin 100 ko dala bilyan 4. 29, daga dala biliyan 33. 02 dake cikinsa a farkon shekara a ranar 2 ga watan Janairun 2024.

Idan kuma aka auna kididdigar shekara zuwa wata, asusun ajiyar Najeriyar na ketare ya bunkasa da kaso 12 cikin 100, inda ya kara dala biliyan 4.03 a kan dala biliyan 33.28 da ake dashi zuwa ranar 18 ga watan Satumbar da muke ciki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG