Babbar kotun jihar Adamawa ta dakatar da majalisar dokokin jihar da cigaba da kokarin tsige gwamnan jihar Murtala Nyako da mataimakinsa James Ngilari.
A hukuncin da kotun ta bayar tace 'yan majalisar basu bi ka'ida ba. Da ma shi gwamnan yayi zargin cewa hanyoyin da 'yan majalisar ke bi basa cikin ka'ida.
Da yake bada umurmin dakatarwar Mukaddashin babban alkalin kotun Ambrose Namadi ya yanke hukuncin cewa wa'adin da doka ta tanada na mako guda na ba gwamnan takardar tuhuma ya wuce.
Malam Ahmed Sajoh daraktan yada labarai na gwamnan yace sun je kotun ne domin hanyar da 'yan majalisa suka bi haramtacciyar hanya ce. Abu na biyu ka'idoji da suka kamata su bi basu bi ba. Abu na uku zarge-zargen da suka yi karerayi ne da tusi barutsu.
Akan zargin cewa gwamnan ya kauracewa ofishinsa sai Malam Sajoh yace ba haka ba ne. Gwamnan ya je aiki ne a Abuja lokacin da tsohon Firayim Ministan Biritaniya Golden Brown ya kai ziyara a jihohi uku dake cikin dokar ta baci.
To saidai 'yan majalisar sun ce suna nan daram akan aniyarsu ta tsige gwamnan. Umaru Sintiri kakakin majalisar yace kawo yanzu babu wata takarda da suka samu daga kotun domin ba'a gayyacesu zuwa kotun ba. Yace komenene ma kotun take son su yi kundun tsarin mulkin kasar ya hana kotu shiga batun tsige gwamna. Domin haka kotu bata da hurumin sa baki. Yanzu suna jira 'yan majalisa su dawo. Duk shawarar da majalisa ta tsayar ita zasu bi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5