Kwana daya bayan da wata Babbar kotu ta wargaza shirin shugaban Amurka Donald Trump ta hanyar kin yarda da tsare iyalan ‘yan gudun hijirar na lokaci mai tsawo, Trump yace warwarewar matsalar naga yan gudun hijirar da kansu.
‘Ku gaya ma mutane kada su kasar mu ba akan ka’ida ba, wannan ita ce mafita, abinda Trump ya gaya wa manema labarai kenan kafin ya hau jirgin shugaban Amurka na Air force one zuwa wani taro da shuwaganannin kungiyar kawancen tsaro ta Nato a Belgium. Shugaban ya yi kira ga masu sha’awar shigowa Amurka su zo Kaman yadda kowa ke zuwa, ta hanyar da ta dace.
Trump kuma ya alakanta karuwar aikata manyan lafufuka a Amurka da shigowar bakin haure, ya kuma jinjinawa jami’an shige da fice da na kwastam na Amurka akan kokarinsu na magance lamarin.
Wani Alkali a babbar kotun birnin Los Angeles dake jihar California ya fada jiya litinin cewar babu wata hujja da zata canza dadaddiyar yarjejeniyar da ta bukaci a ajiye kananan yara a wasu cibiyoyi masu lasi cikin kwanaki 20.