Jiya Jumma'a kasar China ta ce ala tilas ta dau matakin ramuwar gayya kan Amurka, bayan da Amurkar ta sa haraji kan kayakin Chinar guda 800 wadanda kudinsu ya kai dala biliyan $34.
China ta ce ta maka harajin ramuwar gayya kan kayakin Amurka guda 545, wadanda su ma kudinsu ya kai dala biliyan $34. Kayakin sun hada da amfanin gona da motoci da kuma albarkatun ruwa, a cewar kamfanin dillancin labaran China Xinhua.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen China Lu Kang, ya ce China na da cikakkiyar hujjar mai da martani ma Amurka saboda irin harajin da ta saka ma ta, wanda a cewarsa zai kawo tangarda a tsarin cinakayyar duniya, ya kuma kawo cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya, a cewar gidan talabijin din China na CCTV.
'Yan sa'o'i gabanin fara aikin harajin da Amurka ta sa kan kayan Chinar, Shugaban Amurka Donald Trump ya kara gargadin yiwuwar ya maka wani harajin kan kayakin China, na kudi dala biliyan 500, wanda shi ne ma kusan jimlar kayakin da China ta shigar Amurka bara.
Facebook Forum